Connect with us

News

Rasha ta yi ikirarin kashe sojojin Ukraine 500

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Ma’aikatar tsaron Rasha ta yi ikirarin kashe sojojin Ukraine 500 jiya da daddare yayin wasu hare-hare ta sama da ta kai a wurare 87 a Ukraine.

Bataliyoyin soji biyu da ke Kharkiv na cikin wuraren da rahotanni suka ce sojin Rasha sun kai wa hari.

Ma’aikatar ta wallafa wani bidiyo a shafinta na intanet da ke nuna wuraren da dakarunta suka kwace daga hannun sojojin kasa na Ukraine.

Bidiyon ya kuma nuna tankokin yaki da wasu motoci.

Bayanai sun nuna cewa sun samu makamai da wasu takardu da sauran kayayyaki na sojojin Ukraine a wuraren.

Advertisement

BBC ba ta iya tabbatar da gaskiyar wannan ikirari ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending