Connect with us

News

Ɗan majalisar Birtaniya ya ajiye muƙaminsa saboda kama shi yana kallon batsa a majalisa

Published

on

Daga Yasir sani abdullahi

Ɗan Majalisar Dokokin Birtaniya, Neil Parish, ya faɗa wa BBC cewa ya sauka daga muƙaminsa bayan ya amsa cewa ya kalli bidiyon batsa sau biyu a cikin majalisar.

Mista Parish – wanda ke wakiltar mazaɓun Tiverton da Honiton da ke Devon – ya ce “yanayi ne na rashin hankali” kuma “ba na alfahari da abin da na aikata”.

Ya ƙara da cewa karon farko tsautsayi ne bayan ya kalli wasu motocin noma, amma karo na biyun da gangan ya yi.

A ranar Juma’a ne jam’iyyar Conservative ta dakatar da shi saboda zargin.

Wasu mata biyu ‘yan majalisa sun yi iƙirarin cewa sun gan shi yana kallon batsa a wayarsa lokacin da yake zaune kusa da su.

Advertisement

“Abin da ya faru shi ne – motocin noma nake kallo, abin dariya. Na shiga wani shafi da ke da irin wannan sunan kuma na ɗan kalla duk da cewa bai kamata ba. Amma laifina – babban laifina – shi ne cewa na sake kallo a wani lokacin daban.”

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending