Labarai
Gwamnan Ekiti Kayode Fayemi ya ƙaddamar da takarar shugaban ƙasa a APC

Daga yasir sani abdullahi
Gwamnan Jihar Ekiti a kudancin Najeriya, Kayode Fayemi, ya ƙaddamar da takarar neman shugabancin ƙasar a ƙarƙashin jam’iyya mai mulki ta APC a babban zaɓe na 2023.
Fayemi wanda shi ne shugaban Ƙungiyar Gwamnoni ta Najeriya, ya ce zai tabbatar da “kyakkyawan shugabanci da haɗin kan ƙasa” idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa.
Gwamnan zai kara da sauran ‘yan takara a A:PC da suka haɗa da Bola Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo waɗanda suka fito daga shiyya ɗaya ta Kudu maso Yamma. Kazalika akwai Gwamnan Kogi Yahaya Bello, da Gwamnan Ebonyi David Umahi, da sauransu.
APC ta sanya ranar 30 ga watan Mayu zuwa 1 ga watan Yuni don gudanar da zaɓukan fid da gwani tsakanin ‘yan takarar.
-
Labarai6 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai2 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai1 day ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
