News
Malami ya ƙaryata labarin cewa ya raba motoci
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Ministan Shari’a kuma Antoni-Janar na Ƙasa, Abubakar Malami ya musanta labaran da su ka yaɗu a jiya na cewa ya raba motoci na-gani-na-faɗa ga magoya bayan sa.
Malami ya ƙaryata labarin ne a yayin wata ganawa da manema labarai jiya Talata a Birnin Kebbi.
A cewar sa” a kwanakin nan ina shan sharri iri-iri, ta sama, ta ƙasa ta tsakiya, wasu a nan cikin gida wasu kuma daga ƙasashen waje. Har da sahrrin cewa wai na raba motoci ga masu tsada ga ƴan jam’iyar APC.
“A matsayina na mutum mai abokai da dama, ko ni, ko su, babu wanda ya raba wata mota ga kowanne wakilin jami’ya a faɗin jihar nan,” in ji shi.
Malami ya kuma suffanta kabarin a matsayin yarfe da kuma sharri.
Ya kuma yi bayanin cewa shi dai ya san ya gana da shugabannin APC a jihar sakamakon amsa kira da ya yi na al’ummar Kebbi kan ya fito takarar gwamna.
Ya kara da cewa, bayan ganawar, babu wani shugaba ko wakili na jam’iya da a ka baiwa kyautar mota.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
