Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta ce sojojin Israila na yakarsu kafada da kafada da dakarun Ukraine.
Sai dai Maria Zakharova ba ta bayyana wata shaida kan zargin da ta ke yi ba.
Kalaman sun sake tayar da husuma tsakanin kasashen biyu, bayan kalaman ministan harkokin wajen Rasha ranar Litinin cewa Adolf Hitler na da jinin Yahudawa.
Dama wasu ƴan asalin Isra’ila na taimakawa sojojin Ukraine a yakin da suke yi da Rasha, amma babu tabbas ko suna cikin rundunar da ta maƙale a ma’aikatar karafa ta Mariupol.
