News
Ganduje Ya Tsayar Da Gawuna a Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano a APC
Daga Maryam Bashir musa
Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya tsayar da Mataimakin sa, Nasir Yusuf Gawuna a matsayin ɗan takarar gwamnan Kano a jam’iyar APC a zaɓen 2023.
Ganduje ya zaɓi Gawuna ne a wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana.
Majiyoyi makusantan gwamnati sun ce masu ruwa da tsakin kuma sun amince da Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, Murtala Sule Garo, ya zama mataimaki a takarar ta Gawuna.
Rahotanni na cewa da ƙyar masu ruwa da tsaki da wasu manya a jihar su ka shawo kan Garo ya amince da yi wa Gawuna mataimaki a takarar.
Ana ganin cewa Garo, a matsayin dan takarar da ya ke da iko da jam’iyar a matakin Kananan Hukumomi, kuma yana samun goyon bayan da mai-ɗakin gwamna.
Wannan matakin baya rasa nasaba da dalilan da yasa jiga jigai daga jam’iyyar ta APC ke sa kafa suna ficewa daga jam’iyyar suna sauya sheka.
Na baya bayan nan shine tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kano, kuma dan majalisar tarayya Rt Hon Alhassan Rurum wanda ya sanar da ficewar sa daga jam’iyyar.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
