Connect with us

News

Goodluck Jonathan bai fita daga PDP ba zuwa yanzu’

Published

on

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan bai fita daga jam’iyyar PDP mai adawa ba, a cewar Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na PDP Debo Ologunagba.

Mista Ologunagba ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana ta cikin shirin Sunrise Daily na kafar talabijin ta Channels TV a yau Juma’a.

Advertisement

Kalaman nasa na zuwa ne yayin da rahotanni ke cewa Jonathan zai miƙa cikakken fom ɗin takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar APC da aka saya masa a makon da ya gabata.

“Ya zuwa yau ɗin nan da nake magana, ba ni da labarin ya fita daga PDP,” a cewar Ologunagba.

Advertisement

“Ina ganin abu ne mai sauƙi na ce har yanzu ɗan PDP ne shi. Idan kuma wani abu ya faru daga baya sai mu yi magana kan haka.”

Sai dai a ranar Alhamis, jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tsohon shugaban ya yanki katin APC tun a baya, kamar yadda shugabannin APC a yankin ƙaramar hukumar da Jonathan ya fito a Jihar Bayelsa suka bayyana mata.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending