News
Sheikh Khalifa bin Zayed: Shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa UAE ya rasu
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Advertisements
Advertisements
Shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa UAE, Sheikh Khalifa bin Zayed ya rasu a ranar Juma’a, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar WAM ya ruwaito.
WAM ya ce shugaban ya rasu ne yana da shekara 73 a duniya.
Tuni kasar ta sanar da makokin kwana 40 inda za a sassauta tutar kasar tun daga ranar Juma’ar 13 ga watan Mayun 2022.
Advertisements
Sannan ta dakatar da aiki a ma’aikatu da hukumomin ƙasar har tsawon kwana uku.
Advertisements
Advertisements
Advertisements
