Connect with us

Sports

Karim Benzema ya yi kan-kan-kan da Raul a yawan cin kwallaye

Published

on

Daga muhammad Muhammad zahraddin

 

Advertisement

 

Karim Benzema ya yi kan-kan-kan da Raul a mataki na biyu a yawan ci wa Real Madrid kwallaye a tarihi.

Advertisement

Benzema ya ci kwallo daga daga 6-0 da Real Madrid ta caskara Levante a wasan mako na 36 a gasar La Liga da suka fafata ranar Alhamis.

Kawo yanzu dan kasar Faransa ya ci wa Real kwallo 323, iri daya da wanda Raul ya zura a raga a kungiyar tsakanin 1994 zuwa 2010.

Advertisement

Cristiano Ronaldo ne kan gaba a yawan ci wa Real Madrid kwallaye a tarihi mai 451.

 

Advertisement

Benzema ya zura 44 a raga a kakar bana, ita ce wadda ya ci kwallaye da yawa a tarihin sana’arsa ta tamauula.

Ya fara ci wa Real kwallo a wasa na uku da ya yi wa kungiyar a fafatawa da Xerez a gasar La Liga a kakar 2009-10 tun daga nan ya dora.
Kawo yanzu ya lashe kofi 21 a Real Madrid da suka hada da Champions Leagues hudu da Club World Cups hudu da European Super Cups uku da La Liga hudu da Copas del Rey biyu da kuma and 4 Spanish Super Cups hudu.

Advertisement

Cikin kwallo 323 ya zura a gasa shida sun hada da 219 a LaLiga, 74 a Champions League, 21 a Copa del Rey, 3 a Club World Cup da kuma 5 a Spanish Super Cup.

Sauran sun hada da daya a European Super Cup. Kuma kungiyoyin da yafi zura musu kwallaye a raga sun hada da Athletic (18), Valencia (15) da kuma Granada (14).

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending