An harbe wani kanar na dakarun juyin juya hali na Iran a wani kisan kai da ba a saba ganin iirnsa ba a Tehran.
Rahotanni sun ce wasu mutum biyu ne a mota suka harbe Kanar Sayad Khodai a kofar gidansa da ke babban birnin kasar.
Kanar Khodai ne babban jami’i da aka kashe a tawagar Iran tun bayan babban masanin kimiyyar da aka kashe a 2020.
Babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan hari ya zuwa yanzu.
