News
Gwamnan Anambra zai ba da ladan miliyan 10 ga wanda ya taimaka wajen kama waɗanda suka cire wa ɗan majalisa kai
Daga Usman Abdullahi jibirin
Gwamnan Jihar Anambra da ke kudancin Najeriya, Charles Soludo, ya yi tayin ba da ladan miliyan 10 ga duk wanda ya taimaka da bayana da za su kai ga kama waɗanda suka kashe ɗan majalisa tare da cire masa kai.
Da yake miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan Ɗan Majalisar Jiha Okey Di Okay, Gwamna Soludo ya ce babu mamaki gungun da suka kai masa hari ne tare da kashe ‘yan sanda uku shekara biyu da suke wuce, su ne kuma suka kashe ɗan majalisar.
A ranar Lahadin da ta gabata ne ƴan bindiga suka sace ɗan majalisar da ake kira da ke wakiltar Aguata ta arewa, mazaɓar Gwamna Chukwuma Chukwuma Soludo.
An yi garkuwa da shi tare da mai yi masa hidima Cyril Chiegboka a kan titin Aguluzigbo da ke Ƙaramar Hukumar Anaocha ta jihar.
Bayanai sun ce an tsinci kansa da aka fille gefen hanya tare da wata wasiƙar da ke umartar gwamnatin Najeriya ta janye dakarun sojanta daga yankin kudu maso gabashin ƙasar, inda ‘yan awaren ƙungiyar IPOB ke kai hare-hare da zimmar kafa ƙasar Biafra.
