Connect with us

News

Ƴan bindiga sun fille kan dan majalisa a Anambra

Published

on

Daga yasir sani abdullahi

An fille kan wani dan majalisar dokokin jihar Anambra, Dr Okechukwu Okoye, wanda aka yi garkuwa da shi tun farko.

Advertisement

A ranar Lahadin da ta gabata ne ƴan bindiga suka sace ɗan majalisar da ake kira “Okey Di Okay” da ke wakiltar Aguata ta arewa, mazaɓan gwamnatin Anambra Farfesa Chukwuma Chukwuma Soludo.

Bayanai sun ce an tsinci kansa da aka fille gefen hanya tare da wata wasiƙa a yankin Amichi a Anambra.

Advertisement

Rundunar ƴan sandan Anambra cikin wata sanarwa game da al’amarin ta ce a yayin gudanar da bincike wasu mutane sun tsinci gawar mutum ba kai, wanda aka tantance gawar ɗan majalisar ce Hon Okechukwu Okoye.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending