Connect with us

News

Rundunar yan sandan sun kama Mota makare da Bama-Bamai a Kano

Published

on

 

Daga Kabiru basiru fulatan

Advertisement

 

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta samu nasarar cafke wata mota makare da na’urorin hada bama-bamai da bindigogi kirar AK-47 guda biyu a Jihar Kano.

Advertisement

Cikin sanarwa da mai magana da yawun

rundunar a Jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ranar Lahadi, ya ce an samu nasarar wannan kamu ne biyo bayan rahoton sirri da suka samu a kan motar.

Advertisement

“A ranar 19/05/2022 muka samu wasu bayanan sirri cewa akwai wata mota kirar Mercedes Benz mai launin toka da ake zargin ta dauko na’urorin hada abubuwan fashewa da bama-bamai.

“Bayanan da muka samu sun nuna cewa motar ta taho ne daga Jihar Jigawa zuwa Jihar Kano.

Advertisement

“Wannan ce ta sanya Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, fsi, nan take ya ta da wata tawagar kwararrun jami’ai da suka hada da masu warware duk wani nau’i na bama-bamai da kuma rundunar Operation Kan Ka Ce Kwabo.

“Da misalin karfe 4:30 na Yammacin wannan rana [Asabar] ce wadanda ake zargin suka yasar da motar a rukunin gidaje na Bubbugaje da ke Karamar Hukumar Kumbotso ta Jihar Kano.

Advertisement

“Wani bincike na fasaha da rundunar ta gudanar ya nuna cewa motar makare take da na’urori da kayayyakin hada abubuwan fashewar.

“An kuma samu bindigogi kirar AK-47 guda biyu, kwanson alburusai guda hudu na bindigar AK-47..”

Advertisement

Sanarwar da SP Kiyawa ya fitar ta ce tuni bincike ya kankama a kan lamarin.

Idan za a iya tunawa, ko a ranar Talatar da ta gabata sai da aka sami fashewar wani abu da ake zargin bam ne a kusa da wata makaranta da ke unguwar Sabon Gari a cikin birnin na Kano, inda aka samu asarar rayuka tara, wasu kuma suka jikkata.

Advertisement

Sai dai a lokacin, ’yan sanda sun tsaya kai da fata cewa wata tukunyar gas ce ta fashe a shagon wani mai walda, ba harin bam ba ne.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending