News
YANZU-YANZU: Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar A.A. Zaura a Kano
Daga kabiru basu fulatan
Wasu ƴan bindiga sun yi awon-gaba da Hajiya Laure Mai-Kunu, mahaifiyar Abdulsalam Abdulkarim Zaura, ɗan takarar kujerar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa na jam’iyar APC.
An sace tsohuwar ne a gidanta da ke garin Zaura a Ƙaramar Hukumar ungoggo da ke Jihar Kano da asubar yau Litinin.
Lamarin ya faru yayin da Zaura, wanda a ka fi sani da A.A. Zaura ke Birnin Tarayya Abuja wajen babban taron APC .
Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin ga Daily Nigerian Hausa, ta bakin kakakinta, SP Abdullahi Haruna Kiyawa.
Ya ce tuni rundunar ta baza jami’anta na ‘Operation Puff Adda’ domin kuɓutar da Hajiya Laure da kuma kama waɗanda su ka yi garkuwar da ita.
Advertisements
