News
Buhari na ganawa da Shugaban APC, Gwamnoni, gabanin Zaɓen Fidda Gwani
Daga Sulaiman ado ahmad
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a daren Lahadi yana ganawa da wasu manyan Jiga-Jigan APC zuwa liyafar cin Abinci a ɗakin taro na Villa, Abuja.
Manyan Jiga-Jigan Jam’iyyar APC sun haɗa da Shugaban Jam’iyyar Sanata Abdullahi Adamu, da tsohon Sakataren Jam’iyyar Bisi Akande, da John Oyegun, da Sakataren Jam’iyyar Sanata Iyiola Omisore, da wasu Gwamnonin APC.
Taron na daga cikin cigaba da tattaunawa da Shugaban Ƙasa ke yi da masu ruwa da tsaki da dama, domin zaɓar Dan Takarar Shugaban Ƙasa ta hanyar Sasanci.
A taron shi da Ƴan Takarar Shugaban Ƙasa a ranar Asabar da daddare, Buhari daya yi kira ga ƴan Takarar dasu zaɓi Ɗan Takarar Shugaban a tsakanin suz, yace zai tattauna da Masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar.
Yace “wannan shine karo na biyu a jere, kuma ina saran zan sake yin taro da masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar.
Wannan sune matakan da ake ɗauka domin tabbatar da cewa haɗin kai da fahimtar Jam’iyyar an tabbatar dashi.
Hakazalika
Wakilai 2315 ne zasuyi zaben fitar da ‘dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyar APC
A ranar talata 7 ga watan nan jam’iyar APC zata gudanar da babban taron ta a Eegle square a babban birnin tarayya Abuja
Kasancewar wanan taron zai Tara wakilan jam’iyar ta APC daga bangare daban-daban na kasar nan hakan yasa wakilinmu yayi nazari domin Sanin ko adadin wakilai nawa zasu je domin yin wanan zaben daga kowani shiya cikin shiyoyi guda shida da muke dasu
Ga yadda abin yake kamar haka
1. 288 daga Kudu maso gabashin Nigeria wato south east
2.411 daga Kudu maso yamma wato (south west)
3. 359 daga Kudu maso kudu wato (south south)
4. 558 daga arewa maso yamma wato (north west)
5. 336 daga arewa maso gabashin Nigeria wato (north east)
6. 363 daga arewa ta tsakiya wato (north Central)
Wadanan sune adadin Wanda zasu wakilci ko wani shiya daga kasar nan domin zaban shugaban kasa a karkashin jam’iyar APC
