News
An rage wa ɗan sandan Najeriya muƙami bayan bidiyonsa da aka gani yana rawa a Tiktok
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Rundunar ƴan sandan Najeriya ta rage wa wani jami’inta muƙami wanda ta kama yana rawa kuma yana rera wata waka da aka bayyana ta ƴan ƙungiyar asiri a wani bidiyo a kafar Tiktok,
Ɗan sandan da aka bayyana sunansa a matsayin Isaac Mathew, an rage masa mukami daga kofur zuwa kurtun ɗan sanda.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sanda, Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
Ya ce rage wa jami’in girman muƙamin da aka yi, ya biyo bayan shari’ar da aka gudanar akansa da kuma bin tsarin doka kafin yanke masa hukuncin laifin da ya aikata.
Ya ce jami’in ya aikata laifin yaɗa ayyukan ƙungiyar asiri da kuma saɓa dokar ƴan sanda ta amfani da kafafen sada zumunta na intanet.
