Connect with us

News

Kwankwaso ba zai kai labari ba a Kano balle a Najeriya- inji Ganduje.

Published

on

Daga yasir sani Abdullah 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ba zai ci zabe a Kano balle ma a Najeriya ba.

Advertisement

Na barwa Barau Jibril takarar Sanata ne saboda masalahar jam’iyya ta -inji Ganduje.

 

Advertisement

Ganduje yace ba wannan ne karon farko da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yake tsayawa takara amma yake gaza yin nasara ba.

 

Advertisement

 

Ganduje ya bayyana haka ta cikin shirin gidan talabijin din TVC na journalists’ hangout a yammacin yau.

Advertisement

 

’’Kwankwaso yayi takarar shugaban kasa a jam’iyar APC bayyi nasara ba yayi a jam’iyar PDP nan ma bayyi nasara ba a shekara ta 2019.

Advertisement

 

A zabe na jihar Kano ma da temakon Atiku Abubakar, yayi takara amma dashi da Atiku suka fadi ko karamar hukumar sa ta kwankwaso bai kawo ba.

Advertisement

 

Ya ce a lokacin da Kwankwaso yayi hadaka da Atiku Abubakar bayyia nasara ba ta yaya a yanzu da ya koma sabuwar jam’iya shi kadai zayyi hakan ba zai taba yiwu ba, a cewar Ganduje.

Advertisement

 

Ganduje ya kara da cewa la’akari da bangaranci da son kai na Kwankwaso da kuma kasancewar Atiku Abubakar yana takara a yanzu wannan wata dama ce ga Jam’iyar APC a jihar Kano tayin nasara a zaben 2023.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending