News
Wani daliget ɗin APC ya rasu a Abuja
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Wani daliget a Najeriya da ya je Abuja babban birnin ƙasar domin halartar zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa a APC ya rasu.
Taron APC: Ƴan sanda sun harba wa ƴan jarida barkonon tsohuwa
Rahotanni sun ce daliget ɗin mai suna Isa Baba-Buji, ɗan asalin Jihar Jigawa ne kuma ya rasu ne a lokacin da yake karya kumallo kafin tafiya dandalin Eagle.
Wasu da suka tabbatar wa BBC da lamarin sun bayyana cewa ana shirin mayar da shi Jigawa domin gudanar da jana’izarsa kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada
Advertisements
