News
Buhari da wasu ‘yan takara sun fice daga wurin zaɓe
Daga yasir sani Abdullah
Jim kaɗan bayan fara kaɗa ƙuri’a a wurin zaɓen fid da gwani na jam’iyyar APC mai mulki, Shugaba Muhammadu Buhari ya fice daga filin taron.
Wani daliget ɗin APC ya rasu a Abuja
Shugaban ya fita tare da Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan – ɗan takara – da Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo – ɗan takara – da kuma Shugaban APC na Ƙasa Abdullahi Adamu.
Sai dai Buhari bai fice ba sai da ya yi jawabi, yana mai roƙon ‘yan ƙasar da “kada ku bari (jam’iyyar adawa) PDP ta mayar da Najeriya baya”.
A gefe guda kuma, tuni jefa ƙuri’a ya yi nisa, inda daliget ke kaɗa wa ‘yan takara 14 ƙuri’a.
Advertisements
