News
Rasha ta karbe wani muhimmin birni a kasar Ukraine
Daga maryam bashir musa
Jami’an sojan Ukraine sun bayyana cewa, Rasha za ta mallaki babban birnin Severodonetsk da ke gabashin kasar baki daya a cikin kwanaki kadan masu zuwa.
Jami’an soji sun ce a halin yanzu yawancin Severodonetsk na karkashin ikon sojojin Rasha.
Dakarun Rasha sun lalata biyu daga Colin gadoji uku da ke tsakanin garuruwan Lysychansk da Severodonetsk kuma suna lalata na uku da harsasai.
Shugaban hukumar soji ta yankin Luhansk Serhiy Hayday ne ya bayyana kafar yada labarai ta CNN hakan..
Hayday ya ce, “Kamar yadda na fahimci suna son yanke Severodonetsk gaba daya kuma su bar shi ba tare da wata dama ta korar mutane ba ko kawo wani makami ko taimako ba,” in ji Hayday, ya kara da cewa yana tsammanin ‘yan Rasha za su jefa duk abin da suke da shi don kwace birnin.
Ya kara da cewa mai yiyuwa ne dakarun Rasha su katse tare da kwace babbar hanyar shiga birnin
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
