Labarai
Gwamna Sani Bello na Neja ya dakatar da haƙar ma’adinai a jihar

Daga kabiru basiru fulatan
Gwamnan Jihar Neja Abubakar Sani Bello ya sanar da dakatar da haƙar ma’adinai a Ƙananan Hukumomin Shiroro da Munya da Rafi.
Gwamnan ya bayyana haka ne biyo bayan harin da ƴan bindiga suka kai wani wurin haƙar ma’adinai da ke ƙauyen Ajata Aboki da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro da ke jihar.
A cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Ahmed Ibrahim Matane ya fitar, sakataren ya ce akwai buƙatar a dakatar da haƙar ma’adinai sakamakon yadda rashin tsaro ke ƙara ƙamari ƴan kwanakin nan.
Ya ce sun lura da cewa wuraren haƙar ma’adinan na jawo masu aikata laifuka waɗanda suke kasancewa barazana ga rayuka da dukiyoyin jama’a.
Ya kuma yi gargaɗin cewa duk waɗanda aka kama suna gudanar da ayyukan haƙar ma’adinai za su yaba wa aya zaƙinta
-
Labarai6 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai2 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai1 day ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
