News
ISWAP ta ɗauki nauyin kai hari gidan yarin Kuje
Daga kabiru basiru fulatan
Ƙungiyar ISWAP da ke iƙirarin jihadi a Yammacin Afrika ta ɗauki nauyin kai hari gidan yarin Kuje da ke babban birnin tarayyar Najeriya Abuja.
A wani saƙo da ƙungiyar ta wallafa a wani shafin intanet da ƙungiyar ta saba yaɗa farfaganda, ƙungiyar ta ce ta saki fursunoni da dama.
An Sake Damke Fursunoni 551 Da Suka Tsere Daga Kurkukun Kuje
Hukumomin Najeriya dai sun ce akwai fursunoni sama da 400 da har yanzu ba a gansu ba tun bayan harin da aka kai gidan yarin.
Advertisements
