Connect with us

News

Buhari ya tafi Daura domin halartar Babbar Sallah

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa birnin Daura da ke Jihar Katsina domin yin bikin Babbar Sallah.

Shugaban kasar ya tafi mahaifarsa ne ranar Juma’a.

Buhari

Shugaba Buhari ya samu tarba daga Sarkin Daura Alhaji Faruk Umar Faruk da wasu sarakunan gargajiya.

Buhari

Buhari ya isa Daura ne kwanaki uku bayan wasu da ba a san ko su wane ne ba sun kai hari kan ayarin motocinsa a kusa da garin Dutsinma na Jihar Katsina.

An kai harin ne kan ayarin motocin da ke dauke da jami’an da ke yi wa shugaban hidima da kuma ‘yan jarida, a cewar sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar.

Sanarwar ta ce shugaban na Najeriya ba ya cikin ayarin motocin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending