Hukumar kula da alhazai ta Najeriya ta bayyana manyan matsaloli da suka jawo aka samu cikas a aikin diban alhazai a bana.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Fatima Sanda Usara, ta sanya wa hannu hukumar ta ce aikin hajjin bana ya kasance mafi wahala da hukumar ba ta taba gani ba, duk da cewa ba a Najeriya kadai aka fuskanci irin wannan matsalar ba.
Ikweremadu: Kotu ta amince wanda zai ba da gudunmawar ƙoda ba yaro ba ne
Hukumar ta ce matsalolin sun kunshi tafiyar hawainiya lokacin neman biza – saboda rashin isassun kudaden tafiya a hannun wasu da zai taimaka musu samun bizar ta hanya mai sauki – da kuma rashin bin ka’ida a zaben maniyyata da suka cancanta su yi aikin Hajjin bana wanda haka ya kawo jinkirin jigilar alhazan, inda a wasu lokutan kuma rashin karfin intanet ya jawo aka dakatar da bayar da bizar.
Sanarwar ta kara da cewa wasu kasashe ma sun fuskanci matsaloli yayin diban alhazansu. Hakan ya sa hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Saudiyya ta kara wa’adin diban alhazai ga wasu kasashe bayan amincewa da kara wa ita ma Najeriya lokaci.
Wasu abubuwa da suka janyo wa Najeriya manyan matsaloli sun ta’allaka ne kan jiragen da ke jigilar alhazai da rashin bin tsare-tsaren jigila da ya janyo soke tashin jirage 25.
Ya zuwa yanzu dai, alhazan Najeriya 40,000 cikin 43,000 aka diba zuwa Saudiyya.
