‘Yan sanda a Saudiyya sun kama wata yar asalin kasar Masar da ta yi fice a shafukan sada zumunta kan zarginta da yada abubuwan lalata da za su iya cutar da al’umma.
Tala Safwan- da ke zaune birnin Riyadh – tana da mabiya miliyan biyar a TikTok da kuma wasu mabiya 800,000 a YouTube.
An Bayyana Sojojin Rundunar Tsaron Shugaban Kasa Da Aka Kashe A Abuja
Wani bidiyon baya-bayan nan da ta wallafa, ya nuna tana raha da wata ƙawarta – inda mabiyanta suka fassara da cewa, akwai alaƙa ta neman junansu.
Wannan ya sa ake caccakar ta a Twitter har aka ƙirƙiri wani maudu’i mai taken: ‘Tala ta cutar da al’umma’.
Tala Safwan ta musanta zargin da ake mata a bidiyon da ta wallafa.
A kwanan baya hukumomin Saudiyya sun yi barazanar daukar matakin shari’a kan Youtube idan har ya ƙi daukar matakin da ya dace kan yada abubuwan da ba su dace ba.
