Connect with us

News

An kori minista a Ghana bayan ta shafe tsawon lokaci ba ta zuwa wajen aiki

Published

on

Sarah Adwoa Safo

Daga Yasir sani Abdullahi

 

 

 

 

Ministar Jinsi ta Ghana Sarah Adwoa Safo ta rasa aikinta bayan ta shafe fiye da shekara ba tare da ta je aiki ba.

Advertisement

 

Fadar gwamnatin ƙasar ba ta bayyana dalilin da ya sa aka kore ta ba a sanarwar da ta fitar, amma akwai yiwuwar saboda daɗewar da ta yi ne ba ta zuwa aiki.

Kotun majistre ta umarci matashi da ya share haraba bisa yunƙurin yin sata

 

Tuni aka naɗa ministan riƙon ƙwarya a ma’aikatar.

 

Advertisement

A baya, Sarah ta nemi izinin hutu daga Shugaban Ƙasa Nana Akufo-Addo wanda ya ƙare tun a watan Agustan shekarar da ta gabata kuma aka tsawaita mata wa’adinsa.

 

Kazalika, matar ta ƙaurace wa majalisar dokokin ƙasar a matsayinta na mai wakiltar Dome Kwabenya da ke Accra babban birnin ƙasar.

 

Ana sa ran nan gaba kaɗan Kakakin Majalisa Alban Bagbin zai gabatar da rubutaccen ƙudiri da zai kai ga ayyana kujerarta a matsayin fanko.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending