News
An daure mai goyon bayan Trump sama da shekara bakwai
DAGA KHADIJA ABDULLAHI MAHMUD
Kotu a Amurka ta daure dan wata kungiyar bata-gari daga jihar Texas, wanda aka same shi da laifin kutse a ginin Majalisar Dokokin Amurka, Capitol, sama da shekara bakwai a gidan yari.
Hukuncin nasa shi ne mafi tsawo da aka yi wa wani da ke da hannu a tarzomar da aka yi a ginin majalisar a shekarar da ta wuce, inda magoya bayan tsohon shugaban kasar Donald Trump suka kai hari a yunkurin sauya sakamakon zaben shugaban kasar.
Ana zargin ‘yan-sintiri da kashe malamin makarantar allo a Jihar Kano
Guy Reffitt ya kuma yi barazanar harbe ‘ya’yansa idan suka sake suka gaya wa hukumar binciken manyan laifuka ta kasar, FBI a game da shi.
Shedar bidiyo da aka duba ta nuna yadda Guy Reffitt yake jagorantar masu tarzomar su hau matattakalar benen daga wajen ginin, a wannan rana ta 6 ga watan Janairun 2021.
Mai shari’ar Dabney Friedrich ta ce kalaman Mista Reffitt da suka nuna yana son hambarar da majalisar abin tayar da hankali ne da ke da nasaba da shifcin gizo.
Haka kuma ta haramta masa alaka da kungiyoyin bata-gari tare da bayar da umarnin a yi masa maganin tabin hankali.
. BBC HAUSA
