Babban Bankin Ingila ya yi gargadi cewa Burtaniya za ta shiga koma bayan tattalin arziki yayin da ya ƙara ƙudin ruwa mafi yawa a shekaru 27.
Yau Za A Soma Buga Gasar Firimiyar Ingila Kaka Ta 22-23
An yi hasashen tattalin arzikin kasar zai tsuke a watanni uku da suka wuce na wannan shekara kuma zai cigaba da tsukewa har zuwa karshen 2023.
Ƙudin ruwa ya karu da 1.75% yayin da bankin yake takalar tsagaita hauhawar farashin kayayyaki, sannan ana hasashen tauyewar tattalin arziki zai zarta 13%.
Gwamnan Bankin Andrew Bailey ya ce a san yadda tsadar rayuwa ya ke da wahala, amma idan ba a ƙara ƙudin ruwa ba, to abun zai taɓarɓare.
Babban dalilin tauyewar tattalin arziki mai yawa da cigaba ɗan kaɗan shi ne tashin farashin makamashi, wanda kutsen Rasha zuwa Ukraine ke jagoranta.
Yanzu magidanta na kashe kusan £300 a wata akan makamashi zuwa watan Oktoba, bankin yayi gargadi.
Wannan koma bayan tattalin arziki da ake jiran isowarsa shine mafi tsawon lokaci da aka ga ci baya tun 2008, lokacin da bankunan Burtania suka fukanci rushewa, lamarin da ya sa aka dena bada rancen kudi.
