Connect with us

News

Ambaliyar ruwa rusa gidaje masu yawa a kauyuka a Kano

Published

on

Rushewar gidaje Kano

DAGA YASIR SANI ABDULLAH 

 

 

 

 

Ambaliyar ruwa ta rusa gidaje masu yawa a ƙauyuka da dama a yankin ƙaramar hukumar Dawakin Kudu da ke jihar Kano, arewa maso yammacin Najeriya.

Advertisement

 

Mamakon ruwan sama da ake yi a kwanaki da dama a jere ne ya yi sanadiyyar ambaliyar tare da rushewar gidajen.

YANZU-YANZU: WAEC ta fitar da sakamakon WASSCE na 2022

 

A yankin ƙaramar hukumar Ajingi ma an sami asarar rayuka tare da asarar dukiyoyi masu yawa.

 

Advertisement

Haka zalika ginin wata makaranata ya faɗa wa wasu ƴan makaranta wanda ya yi sanadiyar mutuwar ɗaya daga cikinsu.

 

Yankuna da dama a Kano dama wasu jihohi a arewacin Najeriya na fuskantar ambaliyar ruwa, saboda mamakon ruwan sama da ake fuskanta a damunar bana.

 

A makon da ya gabata ms an sheafe kwana uku a jere ana tafka ruwan sama, babu ƙaƙƙautawa, wanda hakan ya shafi harkokin kasuwanci da matsugunan al’umma.

 

Advertisement

A kauyen Shuwawa da ke yankin Danbagina a Dawakin Kudu, da dama daga cikin mazauna ƙauyen sun bar gida, inda suka tura iyalansu gidajen iyayensu, kamar dai yadda Malam Garba Dawa ya shaida wa BBC.

 

Malam Garba ya ce ambaliyar ta rushe gidansa tare da lalata masa amfanin gonarsa baki daya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending