Connect with us

News

GUDUN FAMFALAƘIN 2023: Tsakanin Atiku, Tinubu, Kwankwaso da Obi, wa yawan masu rajista zai fi yi wa tasiri?

Published

on

 

DAGA KHADIJA ABDULLAHI MAHMUD 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana kammala ci gaba da rajistar mallakar katin zaɓe da ta ke yi, bayan an samu sabbin masu rajista mutum miliyan 12 da ɗoriya, tun bayan buɗe ci gaba da yin rajistar a ranar 28 Ga Yuni, 2020.

 

Advertisement

Akwai batutuwa da dama dangane da Rajistar Mallakar Katin Zaɓen da INEC ta kammala.

 

Advertisement

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce ya yi sabbin jarista ga mutane 12, 298, 944. Kafin nan akwai masu rajista har mutane 84, 000, 484. Wato a yanzu akwai waɗanda su ka yi rajista har 96, 299, 428 kenan.

 

Advertisement

Yunƙurowar Matasa Mallakar Katin Zaɓe:

 

Advertisement

Kashi 70 bisa 100 na sabbin masu mallakar katin zaɓe, duk matasa ne. Matasa miliyan 8.7 ne masu shekaru daga 18 zuwa 34 aka yi wa rajista kwanan nan. Masu shekaru 35 zuwa 49 kuwa an samu miliyan 2.4. Sai kuma mutum 856, 017 masu shekaru daga 50 zuwa 69. Masu shekaru 70 zuwa sama kuwa an samu mutum 127, 541.

Hukumar EFCC ta gurfanar da wani mutum da laifin zamba a Abuja

Advertisement

Ba abin mamaki ba ne don an samu matasa da yawa a cikin adadin masu mallakar rajistar katin zaɓe, saboda dama an fito da shirin ne domin waɗanda su ka cika shekaru 18 abin da ya yi sama, bayan 2018 su mallaki katin rajistar zaɓe. Amma fa duk da haka, matasa fa sun yunƙuro.

 

Advertisement

Matan da aka yi wa rajista sun kai 6, 224, 866. Maza kuma 6, 074, 078.

 

Advertisement

Har Yanzu Kano Da Legas Ke Da Mafi Yawan Masu Rajista:

 

Advertisement

Jihohi uku da ke kan gaba wajen yawan waɗanda su ka rajista kwanan nan, sun haɗa da: Legas mutum 585,629. Sai Kano mai 569, 103. Ta uku Delta mai 523, 517.

 

Advertisement

Jihohi masu ƙarancin waɗanda su ka yi rajista kwanan nan, su ne: Ekiti mutum 124, 844. Mai bi mata Jihar Yobe mai 152, 414. Sai Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja mai 211, 341.

 

Advertisement

Tabbas mutum miliyan 12 ɗin da INEC ta ce an ƙara samu sun yi rajista, sun gaza ga miliyan 20 zuwa miliyan 36 da INEC ta ci burin tunanin samu tun da farkon fara ƙarin yin rajistar. Saboda INEC ta sa ran samun aƙalla masu rajista har miliyan 120 kafin zaɓen 2023.

 

Advertisement

Wannan adadin waɗanda su ka yi rajista zai ragu idan INEC ta yi tankaɗe da rairayar waɗanda su ka yi rajista sau biyu ko sama da sau biyu, sai kuma waɗanda su ka yi rajista ba daidai ba.

 

Advertisement

Waɗanda su ka yi rajista daga Janairu zuwa Yuni za su samu katin su cikin Oktoba.

 

Advertisement

Waɗanda su ka yi rajista daga 1 Ga Yuli zuwa 31 Ga Yuli, za su karɓi katin su cikin Nuwamba.

 

Advertisement

Yankin Arewa maso Yamma, wanda ya ƙunshi jihohin Kano, Jigawa, Katsina, Kaduna, Zamfara, Sokoto da Kebbi ne mafi yawan masu rajista har miliyan 22.67.

 

Advertisement

Yankin Kudu maso Yamma, mai jihohin Ekiti, Ondo, Oyo, Ogun, Osun da Legas ne na biyu da masu rajista miliyan 18.3.

 

Advertisement

Kudu maso Kudu mai jihohin Delta, Bayelsa, Edo, Ribas, Cross River da Akwa Ibom ne na uku da rajista miliyan 15.2.

 

Advertisement

Na haɗu a yawan masu rajista shi ne Yankin Arewa ta Tsakiya mai miliyan 14.1. Su ne jihohin Neja, Filato, Nasarawa, Benuwai da FCT.

 

Advertisement

Arewa maso Gabas mai jihohin Adanawa, Barno, Bauchi, Gombe, Yobe da Taraba ne na biyar masu rajaista miliyan 12.8.

 

Advertisement

Kudu maso Gabas da ya haɗa Abiya, Enugu, Imo, Ebonyi da Anambra ne na shida mai rajista miliyan 11.49.

 

Advertisement

Ta Yaya Yawan Masu Rajistar Zaɓe Zai Yi Wa Atiku, Tinubu, Kwankwaso Da Obi Tasiri A Zaɓen 2023:

 

Advertisement

Daga bibiyar yawan masu rajistar zaɓe, za a fahimci ‘yan takarar jam’iyyar APC da PDP har yanzu su ne a sahun gaban yiwuwar lashe zaɓe. Amma fa ƙarfin yunƙurowar da Kwankwaso na NNPP da Obi na LP ya yi, za su iya kawo wa nasarar Atiku cikas sosai. Haka kuma za su iya hana Tinubu lashe zaɓe.

 

Advertisement

Sakamakon zaɓen Ekiti da Osun na gwamna da kuma zaɓukan cike gurabu na jihohi da tarayya sun nuna APC da PDP dai ne manyan ‘yan takara.

 

Advertisement

Yadda Kwankwaso Da Obi Za Su Iya Kayar Da Dawakan Da Tinubu Ko Atiku Ke Sukuwa A Kai:

 

Advertisement

Idan aka duba tsaf, za a fahimci cewa tun bayan kafuwar NNPP ko kuma a ce shigar Kwankwaso NNPP, gaba ɗaya sai tasirin PDP ya mutu a Kano. Haka ita ma jam’iyya mai mulki a Kano ta kasa tsayawa da ƙafafuwan ta ƙyam tun bayan fantsamar wasu jiga-jigan ta cikin NNPP.

 

Advertisement

Kasancewa a Kano aka fi yawan samun ƙuri’u a lokutan zaɓe, hakan na nuni da cewa Kwankwaso zai yi wa APC da PDP kisan-mummuƙe a Kano.

 

Advertisement

Zaɓen 2023 zai zama duk wanda bai ci Kano, Legas ko Kaduna ba, to zai yi wahala ya lashe zaɓen 2023.

 

Advertisement

A Kano dai NNPP ta yi wa APC da PDP Illa. A Kaduna Gwamna Nasir El-Rufai ana ganin ya janyo wa APC baƙin jini. Sannan kuma ɗan jihar Kaduna ne mataimakin takarar Peter Obi na LP.

 

Advertisement

A Kudu maso Kudu kuwa APC ba ta da tasiri. Sun so a ce Gwamna Wike ne ɗan takarar PDP ba Atiku Abubakar ba. Dalili kenan PDP ta kasa barci ta na so sai ta lallashi Gwamna Nysome Wike daga fushin da ya yi. Dama kuma yankin na PDP ne.

 

Advertisement

Rashin bai wa ɗan Kudu maso Gabas takara da PDP ko APC su ka yi, ya sa jihohin Igbo sun karkata ga ɗan su Peter Obi na LP.

 

Advertisement

2023: Ta Ɗan Arewan Ce Ko Ta Ɗan Kudun Ce?

 

Advertisement

Yayin da APC ke taƙama ta na da gwamnoni 14 daga cikin 22 duk a Arewa. Ta na ganin wannan ƙarin ƙarfin ta ne a lokacin zaɓe. Sannan kuma ɗan takarar ta ɗan Kudu ne.

 

Advertisement

Sai dai kuma matsalar da APC ka iya fuskanta ita ce rashin tsayar da Kirista takarar matainakin shugaban ƙasa daga Arewa. Wannan abu hatta Kiristoci daga Kudu da dama bai yi masu daɗi ba.

 

Advertisement

A Arewa kuwa manyan ‘yan APC daga ɓangaren Kiristoci na ci gaba da yin fatali da ɗaukar Kashim Shettima matsayin mataimakin takarar Bola Tinubu na APC.

 

Advertisement

Tasirin Malaman Addini A Zaɓen 2023:

 

Advertisement

Ana ci gaba da yaɗa fatawoyin malamai a Facebook, WhatsApp, Instagram da TikTok, inda yawanci su ke bayyana wa mabiyan su wanda ya fi cancanta a zaɓa.

 

Advertisement

Da yawa daga cikin su kuwa ba su karkata kan Atiku ko Tinubu ba.

 

Advertisement

Haka nan su ma a Kudancin ƙasar nan ba a bar limaman coci-coci a baya ba wajen yaɗa farfagandar wanda su ke ganin ya fi cancanta a zaɓa ba.

 

Advertisement

Ko Farin Jinin Buhariyya Zai Yi Amfani A 2023 Kuwa?:

 

Advertisement

Yayin da zaɓen zai yi zafi wajen tsaren fifikon yawan ƙuri’u a Arewa maso Gabas, inda Atiku na PDP ya fito da kuma Kashin Shettima mataimakin takarar APC, a Arewa ta Tsakiya ma za a gwabza sosai, musamman a Benuwai, Filato da sauran jihohin.

 

Advertisement

Sai dai kuma batun farin jini ko rashin farin jinin Buhari zai iya dagula sakamakon zaɓe a Arewa arankatakaf.

 

Advertisement

Wannan ne zai zama karo na farko babu sunan Buhari cikin ‘yan takara tsawon shekaru 20.

 

Advertisement

Shin ko farin jinin Buhari zai iya sa APC ta samu ƙuri’u miliyan 12 a Arewa maso Yamma kamar yadda Buhari ya samu a 2019? Shin Tinubu zai iya samun hana a 2023?

 

Advertisement

Babbar matsalar da APC za ta samu a Arewa maso Yamma, yankin da ya fi yawan ƙuri’u ita ce matsalar tsaron da ta ragargaza yankin. Mutane da yawa sun dawo daga rakiyar APC, ganin yadda ‘yan bindiga su ka ragargaji Katsina, Zamfara, Kaduna, Sokoto. To shin za su nuna fushin su kan Tinubu, ko kuwa zaɓen sa za su yi?

 

Advertisement

Ko APC Za Ta Ƙara Yin Tazarce Kuwa:

 

Advertisement

Yayin da PDP ta rikito daga kan mulki bayan shekaru 16, yanzu kuma APC da ta rikito da PDP ɗin a ƙasa cikin 2015, ta na fuskantar barazanar neman ita ma a rikito da ita ƙasa a zaben 2023.

 

Advertisement

Amsar wannan tambayar ya dogara ne ga darasin da aka koya daga mulkin APC na tsawon shekaru bakwai. Shin tsaro, tattalin arziki da rashawa da cin hanci sun inganta? An samu ci gaban ilmi a waɗannan shekaru kuwa?

 

Advertisement

Ko me kenan dai za mu ga waɗannan amsoshin a cikin akwatunan zaɓen shugaban ƙasa a 2023.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

PREMIUM TIME

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending