Connect with us

News

An yi jana’izar sojojin rundunar da ke kare shugaban kasa da aka kashe a Abuja

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta binne sojoji biyar da ke rundunar kare shugaban kasa wadanda ‘yan bindiga suka kashe a kwanakin baya.

Advertisement

An binne sojojin ne a makabartar Guards Brigade da ke Maitama , Abuja, a cewar sanarwar da kakakin rundunar, Kyaftin Godfrey Anebi Abakpa

Cikin wadanda aka binne har da Kyaftin Attah Samuel.

Advertisement

“Kafin rasuwarsu, sojojin suna aiki a Bataliya ta 7 da ke barikin Lungi da ke Maitama da Bataliya ta 176 da ke Gwagwalada a birnin tarayya Abuja,” a cewar sanarwar.

Shugaban rundunar Laftanar Kanar Salim Yusuf Hassan ya bayyana Kyaftin din da kuma sauran sojojin a matsayin kwararru a fanninsu kuma sun jajirce wajen kare martabar Najeriya.

Advertisement

A watan jiya ne wasu ‘yan bindiga suka yi wa sojojin kwanton-bauna a yankin Bwari da ke Abuja inda suka kashe su.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending