Labarai
FBI ta gano takardun sirrin kasa a gidan Trump

Daga yasir sani abdullahi
Bayanai game da binciken da FBI ta gudanar a gidan tsohon shugaban Amurka Donald Trump ranar Litinin a Florida sun nuna cewa hukumar ta gano wasu takardu har kashi 11, wasunsu kuma dauke da bayanan tsantsar sirri na kasar.
Bayanan sun ce makasudin samamen na FBI shi ne kan zargin da ake wa Trump din da karya dokokin leken asiri na Amurka, wanda ya shafi ajiye takardu masu matukar muhimmanci ga kasa.
Wadanda ya kamata su kasance a wata ma’ajiya da ke karkashin gwamnati ita kadai.
Wakiliyar BBC ta ce FBI ta je Mar a Logo gidan tsohon shugaba Donald Trump, inda ta bincike dakuna kwana 58, da ban-daki 33.
Wani alkalin Amurka ne ya fallasa bayanan da ke kunshe a takardar, bayan da tsohon shugaban kasar ya ce ba zai hana a fitar da bayanan ba.
A martaninsa ta shafinsa na sada zumunta, Donald Trump ya ce, ya ajiye takardun ne a wata ma’ajiya mai tsaro, kuma a cewarsa zai iya mika su ga hukumar inda sun bukata cikin lalama, ba sai sun sanya siyasa cikin lamarin ta hanyar kai samame a gidansa ba.
-
Labarai6 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai2 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai1 day ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
