Connect with us

News

Salman Rushdie na cikin yanayin rai-fakwai mutu-fakwai

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Sanannen marubucin nan na Burtaniya Salman Rushdie na can a wani asibiti da ke Amurka an makala masa na’urar taimako wajen numfashi, bayan ya samu raunuka sanadiyyar harin da aka kai masa da wuka a birnin New York.

Advertisement

Wakiliyar BBC ta ce wakilin Sir Salman, Andrew Wylie ya ce Salman ya samu rauni a hantarsa, ba zai iya magana ba, kuma akwai yiwuwar zai rasa idonsa daya, yayin da kuma aka yi masa mummunar yanka a wani bangare na hannunsa.

Wani mutum ne dai ya rinka sossoka masa wuka a daidai lokacin da ya hau dandamali domin yin jawabi kan ‘yancin fasaha a wata cibiyar zane-zane.

Advertisement

Salman Rushdie dai ya rinka fuskantar barazana ga rayuwarsa daga wadanda ake ma kallon masu tsattsaurar akidar musulunci tun a shekarar 1989, lokacin da tsohon jagoran Iran, marigayi Ayatollah Khomeini ya bayar da fatawar yin Allah-wadai da littafin da ya rubuta mai taken ‘Satanic Verses’, wanda ake ma kallon wani mummunan sabo.

‘Yansanda sun ce sunan wanda ya kai wa Salman wannan hari Hadi Matar, daga jihar New Jersey.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending