News
Rashin Tsaro: An gudanar da saukar Alkur’ani 2,444 a Kano
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Mahaddata alkur’ani da dama ne suka hadu a masallacin juma’a na Sheikh Ishaq Rabiu da ke Goron Dutse domin yiwa kasa addua saboda matsalar tsaro.
Malaman sun gudanar da saukar Alkur’ani mai tsarki 2,444 tare da addu’ar neman zaman lafiya a Kano da ma kasa baki daya.
An dai gudanar da taron addu’ar ne, karkashin jagorancin Khalifa Nafi’u Ishaq Rabiu.
Da yake jawabi jim kadan bayan kammala karatun, gwani Yusuf Ishaq Rabi’u ya ce babu wata matsala da za ta tunkari jama’a da alkur’ani ba zai magance ta ba.
A don hakan ne ma ya bukaci masu hannu da shuni da ‘yan siyasa su dinga shirya irin wadannan taruka domin nemawa kasa zaman lafiya.
Ya kuma godewa malaman da suka gabatar da sauka tare da bawa al’umma ƙarfin gwiwar cewa Allah zai karbi bukatunsu.
