Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bai wa kamfanonin sufurin jirgin sama na ƙasashen waje kuɗinsu dala miliyan 265 bayan shafe watanni ba sa iya fitar da kuɗin zuwa gida.
Bayanan kuɗin da aka saki ranar Juma’a sun nuna cewa an ba da dala miliyan 230 a matsayin tallafi na kuɗin ƙasar waje, yayin da aka ba da miliyan 35 a wani matsayin daban.
NBC ta janye dakatarwar da ta yi wa kafofin yaɗa labarai a Najeriya
Shugaban sashen hulɗa da jama’a na CBN, Osita Nwanisobi, ya ce Gwamnan CBN Godwin Emefiele da tawagarsa sun damu da halin da ake ciki da kuma halin da ɓangaren sufurin jiragen sama zai shiga a Najeriya.
Nwanisobi ya ƙara da cewa CBN ba ya adawa da kowane kamfani da ke son kwashe kuɗinsa daga Najeriya zuwa ƙasarsa ta asali, yana mai cewa “bankin ya dage ne kan bin doka wajen kwashe kuɗin”.
Sakin kuɗin zai sanyaya zuciyar kamfanonin yayin da tuni wasu daga cikinsu suka rage shiga Najeriya kan hakan, wasu kuma suna shirin daina zuwa baki ɗaya.
Kuɗaɗen na sayen tikiti ne da ‘yan Najeriya da sauran matafiya ke saya da kuɗin naira, inda shi kuma CBN yake bai wa kamfanonin adadin kuɗin a dalar Amurka.

