News
NBC ta janye dakatarwar da ta yi wa kafofin yaɗa labarai a Najeriya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar kula da kafofin yada labarai ta kasa a Najeriya ta janye matakin dakatarwar da ta yi na rufe wasu kafofin yaɗa labarai a kasar saboda kasa sabunta lasisinsu.
Shugaban hukumar, Balarabe Shehu Ilelah, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Juma’a.
Ƴan kasuwar Kantin Kwari sun tafka asarar miliyoyin Naira sakamakon ambaliyar ruwa
A ranar Juma’a, 19 ga watan Agustan 2022 ne hukumar ta kwace lasisin kafofin yada labarai sama da 50, wadanda suka kunshi kafar sadarwa ta DAAR da gidan talabijin na Silverbird da Rhythm FM, saboda bashin da take bin su.
Matakin ya jawo suka ga hukumar wadda a kwanan nan ta ci tarar kafar labarai ta Media Trust naira miliyan biyar da wasu kamfanonin tauraron ɗan Adam kan fim ɗin da suka haska game da ‘yan fashin daji a Jihar Zamfara.
Ilelah ya ce ya samu kyakkyawan martani daga tashoshin yada labaran da ba su sabunta lasisin nasu ba, wanda ya hada da manyan kafofin yada labarai cikin kasar.
“Bayan tattaunawa da jagororin kungiyar masu kafofin yada labarai da kuma sauran masu ruwa da tsaki a bangaren, mun dauki matakin dakatar da bukatar rufe wasu gidajen labaran a fadin kasar.” in ji Ilelah.
