News
YAU TAKE RANAR HAUSA TA DUNIYAR MU: Fadi alkhairi a wannan rana mune kan Gaba🙋
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Muna murna da Dogaro ga Allah maɗaukakin Sarki Da ya rayamu ba waninsa ba.
Al’ummar Hausa ta Hausawa Mu nufi kowa da alheri zaman lafiya ba da sharri ba.
Mu tashi mu gyara al’adu da ɗabi’u karamcin da aka sanmu dashi ba muyi ɓarna ba.
Mu haɗa kanmu duniya ta sanmu harshenmu na Hausa yayi nisa ba yawan kuka ba.
NBC ta janye dakatarwar da ta yi wa kafofin yaɗa labarai a Najeriya
Kowa ya tashi an sanmu da Sana’oin Dogaro dakai ko’ina ba zaman banza ba.
A duba makoma mutumci da karamcinmu da suturunmu na Hausa ba rusa gobe ba.
In muka farka adabinmu da zantukanmu su inganta tabbas ba zamuyi kuka ba.
Kowa ya duba Hausa ta Zama Babban Harshe a duniya kowa ya santa bada jayayya ba.
‘A shuka khairan Hausawa a wannan rana muyi abin alfahari ba ruguza Harshen ba.
Mu mika Komai ga Allah shi ya ɗaukaka Hausa da Hausawa Ba da Gazawa ba.
Duk zamu rabauta da Hausarmu muna tunkaho
A Duniya ba zamuyi nadama ba.
