News
Ana zanga-zangar nuna goyon baya ga mataimakiyar shugabar Argentina
DAGA MARHAM BASHIR MUSA
Dubban mutane ne suka bazama kan tituna a Argentina inda suke goyon bayan mataimakiyar shugabar ƙasar Cristina Fernandez de Katchner wadda take fuskantar tuhume-tuhume na cin hanci.
A Bonezairez babban birnin ƙasar, wasu tarin magoya bayanta ne suka taru a gaban gidanta inda suka rinƙa arangama da jami’an tsaro inda suka rinƙa tutture shingayen da aka saka na hana taruwar jama’a.
Farashin Masara Ya Fadi Kasa Warwas A Arewa
A makon da ya gabata, masu shigar da ƙara na kasar sun zarge ta da damfarar ƙasar da kuma zarginta da hannu a wani tsari wanda aka karkatar da kuɗaɗen ƙasar a lokacin da ta shugabancin Argentinar tsakanin 2007 zuwa 2015.
Masu shigar da ƙara a ƙasar na neman a hana ta riƙe duk wani muƙami a ƙasar da kuma rufe ta a gidan yari tsawon shekara 12, sai dai Ms Katchner ɗin ta musanta zarge-zargen da ake tuhumarta da su.
BBC NEWS
