News
YANZU-YANZU: Atiku ya sauka a Kano domin karɓar Shekarau zuwa PDP
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma dan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar ya isa Kano.
Atiku, wanda ya samu rakiyar abokin takararsa Gwamna Ifeanyi Okowa, shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu ya tare shi, ya je Kano domin tarbar tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Shekarau zuwa jam’iyyar PDP.
Rikicin gwamnatoci masu adawa a Libya ya kashe mutum 32
Atiku ya bayyana zuwan sa ne a wani sako da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta a yau Lahadi.
Ya ce: “Na zo cibiyar kasuwanci ta jihar Kano. Kwanaki masu zuwa za su zama na gwagwarmaya.AA #AtikuInKano,” in ji Atiku.
Advertisements
