Connect with us

News

Rikicin gwamnatoci masu adawa a Libya ya kashe mutum 32

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

 

 

 

Advertisement

 

 

Rikici tsakanin ƙungiyoyin da ke biyayya ga gwamnatocin Libya biyu ya yi sanadiyyar kashe mutum 32, a cewar ma’aikatar lafiya ranar Lahadi, sakamakon faɗan da ya ɓarke a baya-bayan nan.

 

Gungun ‘yan bindiga sun yi ta ɓarin wuta da ya lalata asibitoci da dama da kuma ƙona gine-gine tun daga ranar Juma’a da yamma, wanda shi ne mafi muni a birnin Tripoli tun bayan yarjejeniyar tsagaita wuta a 2020.

Pogba na fuskantar ‘kwace da barazana’ daga wata kungiyar masu laifi

Advertisement

Ƙura ta ɗan lafa ya zuwa Asabar da dare, a cewar wakilin kamfanin labarai na AFP.

 

Faɗan ya ɓarke ne bayan cecekuce tsakanin magoya bayan Abdulhamid Dbeibah da na Fathi Bashagha da ke jagorancin gwamnatoci daban-daban kuma suke neman iko da yankunan ƙasar da ke arewacin Afirka.

 

Gwamnatin Dbeibah da aka kafa a Tripoli a matsayin wani ɓangare na yunƙurin zaman lafiya ƙarƙashin shirin Majalisar Ɗinkin Duniya, ta hana Bashagha shiga ofis a can tana mai cewa dole sai an gudanar da zaɓe.

 

Advertisement

Tun bayan kashe Muammar Gaddafi a 2011, Libya ba ta sake samun cikakkiyar gwamnati ba, inda tashin hankali ya fi zaman lafiya yawa.

 

. BBC NEWS

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending