Connect with us

News

Babu ɗan takarar da nake mara wa baya a zaɓen shugaban ƙasa – Obasanjo

Published

on

Obasanjo

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce babu ɗan takarar shugaban ƙasa da yake mara wa baya a babban zaɓen ƙasar na 2023 da ke tafe, a cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Advertisement

 

Da yake magana a Minna, babban birnin Jihar Neja yayin ziyarar da ya kai wa Tsohon Shugaban Mulkin Soja Badamasi Babangida ranar Lahadi, Obasanjo ya ce Najeriya ce a gabansa ba wani ɗan takara ba.

Advertisement

Ibrahim Ahmad: Makahon Da Ke Saka Kayan Adon Daki

“Ba ni da ɗan takara, ƙasa ce a gabana,” in ji shi. “Na zo ziyarar ɗan uwana da ya yi ‘yar rashin lafiya, wanda na so na yi hakan tun yana Landan amma sai ya koma gida a ranar da na isa Landan ɗin.”

Advertisement

 

A makon da ya gabata, an ga Obasanjo a birnin Landan na ganawa da ɗan takarar jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, da sauran ‘yan siyasa. Kafin haka, ɗan takarar APC, Bola Tinubu, ya ziyarce shi a birnin Abeokuta na Jihar Ogun.

Advertisement

 

Bisa al’ada, akasarin masu neman shugabancin Najeriya kan kai wa tsofaffin shugabannin ziyara don neman goyon bayansu a kowace shekarar zaɓe.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending