Connect with us

News

Gwamna Mai Mals Buni Ya Bude Kasuwar Zamanin Daya Gina A Karamar Hukumar Gashua

Published

on

Buni

 

Daga Idriss Hussain Nguru

 

 

 

 

Advertisement

 

 

 

 

 

Gwamna Mai Mals Buni Ya Bude Kasuwar Zamanin Daya Gina A Karamar Hukumar Gashua

Advertisement

Gashua, hedkwatar karamar hukumar Bade a ranar Asabar din da ta gabata ta tsaya cak ga shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan da gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, yayin da dubban jama’a suka yi dafifi a sabuwar kasuwar Gashua da aka gina domin shaida bikin kaddamar da kasuwar.

Da yake jawabi tun da farko, Gwamna mai mala Buni ya sanar da sanyawa kasuwar karfin shaguna 505 sunan shugaban majalisar dattawa.

Mai mala buni ya ce, sanya wa kasuwar sunan Sanata Ahmed Lawan, ya kasance ne don karramawa da kuma yabawa irin gudunmawar da ya bayar a jihar, Arewa maso Gabas da Nijeriya.

Gwamna mai mala Buni ya yabawa shugaban majalisar dattawan bisa kara jan hankalin gwamnatin tarayya zuwa jihar.

Yayin kaddamar da kasuwar, Sanata Ahmed Lawan ya yabawa gwamnatin jihar Yobe bisa karramawar da aka yi masa, ya kuma yi alkawarin kara yin hakan.

Ya ce yabo na musamman ne ya zaburar da shi, kuma zai ci gaba da yi wa jiha da kasa hidima tukuru.

Advertisement

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed lawan PhD con, ya baiwa ‘yan kasuwa 400 tallafin Naira miliyan 200 domin bunkasa kasuwancinsu.

Taron ya samu halartar dubunnan masoya da magoya baya daga ciki da wajen jihar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending