Connect with us

Sports

An caccaki kociyan PSG da dan wasanta Mbappe

Published

on

DAGA YASIR SANJ ABDULLAHI 

 

Ana ta caccakar Paris St-Germain, bayan kalaman raha da aka yi kan shatar jirgin sama idan za su yi wasan da za su buga a waje mara nisa.

Advertisement

Hakan ya biyo amsar da babban cociyan kungiyar Christophe Galtier da dan wasa Kylian Mbappe suka bayar lokacin da aka yi musu tambaya kan balaguron da suka yi shatar jirgin sama zuwa yammacin birnin Nantes.

Najeriya da Poland sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Samar da Abinci

Advertisement

A lokacin ne Mbappe ya bushe da dariya – shi kuma Galtier ya kada baki ya ce kulub din ya na duba yiwuwar balaguro ta amfani da jirgin ruwa mai tafiya a yashi, maimakon jirgin sama.

‘Yan siyasar Faransa sun gargadi PSG ta maida hankali ta dauki batun muhalli da muhimmanci.

Advertisement

PSG ta zura kwallo 3 a ragar Nantes a wasan da suka kara ranar Asabar, amma sai ranar Lahadi sannan barkwancin ya fito, lokacin da babban jami’in sufurin jirgin kasa na Faransa SNCF ya wallafa a shafinsa na tiwita cewa: “Daga birnin Prais zuwa Nantes tafiyar awa biyu ta amfani da jirgin kasa mai gudun gaske.

A lokacin da aka tambayi Galtier da Mbappé a taron manema labarai ranar Litinin, kawai sai dan wasan ya bushe da dariya, ya yin da shi kuma Galtier ya maida martani da cewa: “Na san daman za ai wannan tambayar”.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending