Sports
Wasannin Da Za A Fafata Ranar Talata A Gasar Zakarun Turai
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
A Yammacin Talatar nan za a soma wasannin farko na cikin rukuni a gasar Zakarun Turai ta kakar 2022/2023.
Wasanni takwas za a fafata tsakanin. kungiyoyin 16, inda kowacce za ta yi kokarin fitowa kwanta da kwarkwarta tana mai fatan samun nasara.
Sabuwar firaministar Burtaniya Liz Truss ta gana da Sarauniya
Wannan ce gasa ta 68 da za a gudanar karo na 31 tun bayan da aka sauya fasalin wasannin.
Real Madrid wacce ita ce kan gaba a bajinta a tarin gasar, ta lashe ta sau 14 kuma ita ce mai rike da kambu a yanzu bayan doke Liverpool da ta yi a fafatawar da suka yi a karkashen kakar da gabata a Faransa.
Yadda kungiyoyin suke a kowane rukuni:
Rukunin A: Ajax, Liverpool, Napoli, Rangers
Rukunin B: Porto, Atletico Madrid, Bayer Leverkusen, Club Bruges
Rukunin C: Bayern Munich, Barcelona, Inter Milan, Viktoria Plzen
Rukunin D: Eintracht Frankfurt, Tottenham, Sporting Lisbon, Marseille
Rukunin E: AC Milan, Chelsea, RB Salzburg, Dinamo Zagreb
Rukunin F: Real Madrid, RB Leipzig, Shakhtar Donetsk, Celtic
Rukunin G: Manchester City, Sevilla, Borussia Dortmund, FC Copenhagen
Rukunin H: Paris St-Germain, Juventus, Benfica, Maccabi Haifa
Wasannin da za a fafata ranar Talata
(Rukunin E)
Dinamo Zageb da Chelsea
Alkali: Istvan Kovacs (Romania)
Wuri: Filin wasa na Stadion Maksimir
Lokaci: 5:30 na Yamma
FC Salzburg da AC Milan
Alkali: Srdjan Jovanovic (Serbia)
Wuri: Red Bull Arena
Lokaci: 8:00 na Yamma
(Rukunin F)
Celtic da Real Madrid
Alkali: Sandro Schaerer (Switzerland)
Wuri: Celtic Park
Lokaci: 8:00 na Yamma
RB Leipzig da Shakhtar Donestk
Alkali: Joao Pinheiro (Portugal)
Wuri: Red Bull Arena Leipzig
Lokaci: 8:00 na Yamma
(Rukunin G)
Borussia Dortmund da FC Copenhagen
Alkali: Francois Letexier (Faransa)
Wuri: Signal Iduna Park
Lokaci: 5:30 na Yamma
Sevilla da Manchester City
Alkali: Davide Massa (Italiya)
Wuri: Estadio R. Sanchez Pizjuan
Lokaci: 8:00 na Yamma
(Rukunin H)
Benfica da Maccabi Haifa
Alkali: Andreas Ekberg (Sweden)
Alkali: Estadio da Luz
Lokaci: 8:00 na Yamma
Paris Saint Germain da Juventus
Alkali: Anthony Taylor (Ingila)
Wuri: Parc des Princes
Lokaci: 8:00 na Yamma
