Sports
Champions League: Abin da ya kamata ku sani kan wasannin Laraba
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Za a ci gaba da wasannin farko a cikin rukuni a Champions League kakar 2022/23, inda za a yi fafatawa takwas ranar Laraba.
Wannan ce gasa ta 68 da za a gudanar karo na 31 tun bayan da aka sauya fasalin wasannin.
Real Madrid ce mai rike da kofin da ta lashe a kakar da ta wuce, mai 14 jumulla ita ce kan gaba a bajinta.
Real ta fara kare kofinta da kafar dama, bayan da ta je ta doke Celtic 3-0 a wasan farko a cikin rukuni ranar Talata.
Rukuni hudu ne zai yi wasannin farko a ranar ta Laraba.
Rukunin farko
Ajax Amsterdam
Liverpool
Napoli
Glasgow Rangers
Za a buga wasa tsakanin Ajax Amsterdam da Glasgow Rangers
Jerin karawa da suka yi a tsakaninsu
1996/1997
Champions League Laraba 30 ga watan Oktoba 1996
- Rangers 0 – 1 Ajax
Champions League Laraba 16 ga watan Octoba 1996
- Ajax 4 – 1 Rangers
1972/1973
European Super Cup Laraba 24 ga watan Janairun 1973
- Ajax 3 – 2 Rangers
European Super Cup Talata 16 ga watan Janairun 1973
- Rangers 1 – 3 Ajax
Daya wasan shi ne tsakanin Napoli da Liverpool
Jerin karawa da suka yi a tsakaninsu
2019/2020
Champions League Laraba 27 ga watan Nuwambar 2019
- Liverpool 1 – 1 Napoli
Champions League Ranar Talata 17 ga watan Satumbar 2019
- Napoli 2 – 0 Liverpool
2018/2019
Champions League Talata 11 ga watan Disambar 2018
- Liverpool 1 – 0 Napoli
Champions League Laraba 3 ga watan Oktoban 2018
- Napoli 1 – 0 Liverpool
2010/2011
Champions League Talata 4 ga watan Nuwambar 2010
- Liverpool 3 – 1 Napoli
Europa League Alhamis 21 ga watan Oktoban 2010
- Napoli 0 – 0 Liverpool
Wannan rukunin Liverpool tana da Champions League shida da Ajax mai hudu.
Rukuni na biyu
FC Porto
Atletico Madrid
Bayer 04 Leverkusen
Club Brugge
Za a buga wasa tsakanin Atletico Madrid da FC Porto
Jerin karawa da suka yi a tsakaninsu
2021/2022
Champions League Talata 7 ga watan Disambar 2021
- Porto 1 – 3 Atl Madrid
Champions League Laraba 15 ga watan Satumbar 2021
- Atl Madrid 0 – 0 Porto
2013/2014
Champions League Laraba 11 ga watan Disambar 2013
- Atl Madrid 2 – 0 Porto
Champions League Talata 1 ga watan Oktoban 2013
- Porto 1 – 2 Atl Madrid
2009/2010
Champions League Talata 8 ga watan Disambar 2009
- Atl Madrid 0 – 3 Porto
Champions League Laraba 30 ga watan Satumbar 2009
- Porto 2 – 0 Atl Madrid
2008/2009
Champions League Laraba 11 ga watan Maris 2009
- Porto 0 – 0 Atl Madrid
Champions League Talata 24 ga watan Fabrairun 2009
- Atl Madrid 2 – 2 Porto
1963/1964
Fairs Cup Laraba 9 ga watan Oktoban 1963
- Porto 0 – 0 Atl Madrid
Fairs Cup Laraba 25 ga watan Satumbar 1963
- Atl Madrid 2 – 1 Porto
Za kuma a fafata tsakanin Club Brugge da Bayer 04 Leverkusen
Wasa daya suka yi a gasar zakarun Turai a tsakaninsu
2006/2007
Uefa CUP Alhamis 19 ga watan Oktoban 2006
- Club Brugge 1 – 1 B Leverkusen
A wannan rukunin FC Porto ce kadai mai Champions League biyu.
Rukuni na uku
FC Bayern Munich
FC Barcelona
FC Viktoria Plzen
Inter Milan
A wannan rukunin Inter Milan za tta karbi bakuncin Bayern Munich
Jerin karawa da suka yi a tsakaninsu
2010/2011
Champions League Talata 15 ga watan Maris 2011
B Munich 2 – 3 Inter
Champions League Laraba 23 ga watan Sabrairun 2011
Inter 0 – 1 B Munich
2009/2010
Champions League Asabar 22 ga watan Mayun 2010
B Munich 0 – 2 Inter
2006/2007
Champions League Talata 5 ga watan Disambar 2006
B Munich 1 – 1 Inter
Champions League Laraba 27 ga watan Satumbar 2006
Inter 0 – 2 B Munich
A wannan rukunin Barcelona da Viktoria Plzen za su kece raini a tsakaninsu
Jerin karawa da suka yi a tsakaninsu
2011/2012
Champions League Talata 1 ga watan Nuwambar 2011
Viktoria Plzen 0 – 4 Barcelona
Champions League Laraba 19 ga watan Oktoban 2011
Barcelona 2 – 0 Viktoria Plzen
A wannan rukunin an lashe Champions League 14, inda Bayern ta dauki shida da Barcelona mai biyar da Inter da ta dauki uku.
Rukuni na hudu
Eintracht Frankfurt
Tottenham
Sporting
Olympique Marseille
Wannan rukunin za a fafatawa tsakanin Eintracht Frankfurt da Sporting.
Haka kuma Tottenham za ta karbi bakuncin Olympique Marseille.
Wannan shi ne karon farko da kungiyoyin za su fuskanci juna a Champions League.
Olympique Marseille ce kadai ta ci Champions League a rukunin nan, wadda ta dauka a 1992/1993 .
Sakamakaoan wasannin da aka buga ranar Talata:
Borussia Dortmund 3 – 0 FC Kobenhavn
Dinamo Zagreb 1 – 0 Chelsea
Sevilla 0 – 4 Manchester City
Paris Saint-Germain 2 – 1 Juventus
Celtic Glasgow 0 – 3 Real Madrid
Benfica 2-0 Maccabi Haifa
Red Bull Salzburg 1 – 1 AC Milan
RB Leipzig 1 – 4 Shakhtar Donetsk
BBC NEWS
