Sports
Ƙwallon mata: Najeriya ta kai wasan kusa da ƙarshe a Kofin Duniya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Ƙungiyar kwallon kafar mata ta Najeriya ta doke takwararta ta Amurka a bugun fenariti da ci 4-3 domin zuwa zagayen kusa da na ƙarshe bayan tashi 1-1 a gasar cin kofin ɗuniya ta mata ‘yan kasa da shekara 17 da ake gudnarwa a Indiya.
Edafe Omamuzo ce ta ci kwallon karshe da ya bai wa matan na Najeriya nasara a birnin Mumbai.
Jirgin Sama Dauke Da Fasinjoji Ya Bace
An dai samu jinkiri sa’a ɓiyu kafin soma buga wasan sakamakon sawa na ruwan sama da aka samu, inda Omamuzo ta fara cin kwallo a minti na 26.
Sai dai takwararta ta Amurka Amalia ta farke musu bayan da kwallon da ta buga ya dagi ‘yar wasan Najeriya kafin shiga raga..
Ɓayan tashi 1-1, sai aka je zuwa bugun fenariti, inda Najeriya ta sami nasara bayan doƙe takwarorinsu mata na Amurka.
