Connect with us

News

CBN na shirin kaddamar da sabon katin biyan kuɗi na bai-ɗaya a Najeriya

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

Advertisement

 

Babban bankin Najeriya CBN ya ce zai ƙaddamar da tsarin katin bai-ɗaya ranar 16 ga watan Janairun 2023.

Advertisement

Za a kaddamar da shirin ne karkashin tsarin yarjejeniyoyi tsakanin bankunan kasar (NIBSS) tare da hadin gwiwwa da kwamitin ma’aikatan banki.

NDLEA ta kama mutum 192 da ake zargi da safarar kwaya

Advertisement

A wata sanarwa da kakakin babban bankin kasar Osita Nwanisobi, ya fitar wanda jaridaun Najeriya suka wallafa, ya ce tsarin zai saukaka kashe kudi tare da rage yawan kudin da ake cazar kwastomomi.

Sanarwar ta ci gaba da cewa ”Najeriya ce kasar ta tafi kowacce karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka, da kuma ci gaba a fannin fasahar zamanantar da abubuwa, kuma a kokarin babban bankin kasar na bunkasa fannin fasahar zamani ne ya sa ya kirkiro da wannan sabuwar fasaha”.

Advertisement

Babban bankin ya ce baya ga bunkasa fasahar zamani a fannin kasuwancin kasar, shirin zai bayar da dama ga bankunan kasar su warware tarin matsalolin da ke musu dabaibayi.

Idan aka kaddamar da shirin Najeriya za ta bi sahun kasashe irin su Indiya da Turkiya da China da Brazil wadanda suka daɗe suna amfani da tsarin katin biyan kuɗi na bai-ɗaya, kamar yadda babban bankin kasar ya bayyana.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending