Connect with us

News

Ƴan daba sun shiga gidan kakakin majalisar wakilai ta Amurka, Pelosi tare da jikkata mijinta

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Wasu ɓatagari sun kutsa kai cikin gidan Kakakin Majalisar Wakilai ta Amurka, Nancy Pelosi, inda su ka jikkata mijinta, Paul Pelosi, wanda ya samu muggan raunuka.

Advertisement

Ofishin Pelosi ɗin ne ya fitar da sanarwar a yau Juma’a.

Ƙarin ƙasashe biyar sun bayyana fargabar harin ta’addanci a Abuja

Advertisement

Sanarwar ta ce “An tsare wanda ya kai harin kuma ana bincike kan dalilin da ya sa ya kai harin.”

“ An garzaya da Pelosi asibiti, inda yake samun kyakkyawar kulawar jinya kuma ana sa ran zai samu cikakkiyar lafiya.”

Advertisement

Jaridar daily Nigerian ta rawaito cewa Kakakin Majalisar ƴar jam’iyyar Democratic, wanda ke matsayin ta biyu a tsarin shugabancin Amurka, ba ta gida a lokacin da aka kai harin da sanyin safiyar yau Juma’a.

A watan Mayu a ka kama Paul Pelosi, mai shekaru 82 da laifin tuki cikin maye bayan, lamarin da ya haifar masa da yin hatsarin mota. An yanke masa hukuncin daurin kwanaki biyar a gidan yari a gundumar Napa da ke California.

Advertisement

Pelosi ne mamallakin wani katafaren rukunin gidaje da kuma babban kamfani na San Francisco.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending