Connect with us

News

Ƙarin ƙasashe biyar sun bayyana fargabar harin ta’addanci a Abuja

Published

on

'Yan sandan Najeriya

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Ƙarin ƙasashe biyar sun bi sahun Amurka da Birtaniya wajen bayyana fargabar kai harin ta’addanci a Abuja babban birnin Najeriya tun daga ƙarshen makon da ya gabata, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Advertisement

 

Amurka ce ta fara bayyana damuwa a ranar Lahadi, tana mai cewa akwai yiwuwar kai hari kan gine-ginen gwamnati da wuraren taruwar jama’a, kafin a ranar Juma’a ta umarci wasu ma’aikatan difilomasiyyarta su fice daga binin tare da iyalansu nan take.

Advertisement

An Sace Tsohon Sakataren Gwamnati A Inugu

Jim kaɗan bayan haka Ofishin Harkokin Waje na Birtaniya ma ya gargaɗi ‘yan ƙasarsa da su ankare kuma su guji yawo a Abuja tare da kauce wa shiga taron jama’a.

Advertisement

 

Ƙasashen Jamus da Bulgeriya da Ireland da Kanada da Denmark sun bi sahu, inda suke cewa akwai yiwuwar ‘yan ta’adda za su kai hare-hare sannan suka nemi ‘yan ƙasashensu su yi taka-tsantsan ko kuma su fice daga birnin.

Advertisement

 

Sai dai Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba ya jaddada cewa babu wata fargabar kai hare-hare a Abuja, bayan ya umarci jami’ansa da su tsaurara tsaro a kewayen Abuja.

Advertisement

 

“Saboda haka IGP na kwantar wa da mazauna Abuja hankali tare da ƙarfafa musu gwiwar ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum yayin da aka shirya tsafi don daƙile barazanar tsaro da kuma amsa kiran gaggawa a kan lokaci,” in ji sanarwar da kakakin ‘yan sandan ya fitar ranar Alhamis.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending