Connect with us

News

An Sace Tsohon Sakataren Gwamnati A Inugu

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

 

 

Yan bindiga sun sace tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Inugu, Dokta Dan Shere, tare da wasu matafiya da ba a tantace adadinsu ba.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne ranar Alhamis a hayar Enugu zuwa Ugwuogo, Nike zuwa Nsukka, a lokacin da Shere ke kan hanyarsa ta dawowa daga wani taro da ya halarta.

Advertisement

Babu barazanar tsaro a Abuja – IGP Usman Alkali

Majiyarmu ta ce ’yan bindigar wanda adadinsu ya kai takwas, sai da suka yi harbe-harben bindiga a iska don razana jama’a kafin daga bisani suka yi garkuwa da su.

Sace mutanen ya jefa jama’ar yankin cikin mummunan tashin hankali, inda suka yi kira ga jami’an tsaro da a gaggauta daukar matakin ceto su.

Shere ya yi Sakataren Gwmanatin jiahr ne a zamanin tsohon Gwamnan Inugu, Chimaroke Nnamani.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending